Duniyar Fina-Finai: Za A Ɗaure Masu Fim Ɗin Maɗigo – Hukumar Tace Fina-Finai

Wasu masu shirya finafinai biyu na fuskantar yiwuwar ɗauri idan suka yi burus da tsattsauran gargaɗin da hukumomi suka yi masu, suka ci gaba da shirye-shiryen fitar da wani fim da ke nuna wasu mata biyu suna soyayya kamar yadda jaridar BBC ta rawaito.

Haska fim

Don samun damar haska fim ɗin, masu shiryawar na shirin fitar da shi a shafukan intanet don yi wa masu sa idon ba-zata. Sai dai NFVCB na matuƙar sa ido kan duka hanyoyin shafukan intanet don hana fim ɗin fita.

A cewar shugaban tace fina-finai ta Najeriya Adebayo Thomas, Adie da Ikpe-Etim na iya shan ɗauri bisa laifin nuna luwaɗi da maɗigo a ƙasar da aka haramta su kuma wanda aka kama da laifin haka na iya zaman gidan kaso tsawon shekaru 14.

Suna shirya haska fim ɗin cikin sirri a birnin Legas a karshen wannan watan, wanda kuma suke ganin za su iya yi ba tare da samun izini ba.

Wacce ta shirya fim din Adie ta ce manufar fim ɗin shi ne a nuna gaskiyar yadda rayuwar ‘yan maɗigo take a fina-finan Najeriya.

Idan aka nuna mace ‘yar maɗigo a fim ɗin Nollywood, ana nuna su a matsayin masu shafar aljannu ko kuma ƙawayen da ba na kirki ba sun ja ra’ayinsu ko kuma an turasasa masu fara maɗigon, sannan ana nuna cewa suna ɓukatar a kuɓutar da su daga wannan hanya, a cewarta.

“Da wuya ka ga labari kan mata ko maza ‘yan luwaɗi, musamman ma mata.

“An haɗa fim ɗin Ife ne don gyara wannan giɓin sannan a sa mutane su fara tattauanawa kan wannan batu a Najeriya.”

‘Dole ne a tantance shi’

Madigo da Luwadi manyan abubuwa ne da ke janyo ce-ce-ku-ce sosai a bangarori da dama a Afrika.

Afrika nahiya ce da addini da al’ada suke da tasiri, kuma addinin Kirista da na Musulunci sun haramta madigo da luwadi.

A dalilin haka, Najeriya na daya daga cikin kasashe 30 a nahiyar da ake kama masu aikata su.

An kafa dokar da ke haramta soyayya ko auren jinsi daya a shekarar 2014 a Najeriya. ‘Yan sanda a kasar sun sha kama wadanda ake zargi da aikata madigo da luwadi, inda mafi yawansu suke buya.

“Idan fim din bai bi ta hannun NFVCB ba kuma aka fitar da shi, masu shirya fina-finan na iya fuskantar dauri,” a cewar Mista Thomas.

“Matsawar a Najeriya aka shirya shi, za mu cire shi saboda muna hada kai da Google da Youtube da sauran masu ruwa da tsaki.”

Amma wannan bai sagar da gwiwowin masu masu shirya fim din ba kuma Adie ta ce tawagarta za ta ci gaba da shirye-shiryenta saboda sun yi amannar cewa ba su aikata wani laifi ba kuma ba za su nemi izinin fitar da fim din a shafukan intanet ba.

Ba wannan ne karon farko da wani fim kan auren jinsi daya ya jawo karawa da hukumomi a nahiyar ba.

An haramta fim din Stories of Our Lives, kan soyayyar jinsi daya a Kenya a 2014 saboda “saba wa dokokin kasa”.

Haka ma fim din Rafiki na Kenya wanda ya nuna mata biyu suna soyayya, wanda ya zama fim na farko a yankin Afrika ta Gabas da aka haska a bikin haska fina-finai na Cannes sannan aka zabe shi a matakin farko a bikin fina-finai na Oscar.

An haramta fim din Inxeba/The Wound na Afrika ta Kudu da ya nuna soyayya tsakanin maza biyu a kasar a shekarar 2018.

Duk da wannan koma bayan, wasu kungiyoyin masu auren jinsi daya a Afrika sun ce suna samun karbuwa a hankali kuma sun danganta haka da bayyana labaransu da ake yi a fina-finai da littafai da ke nuna amfaninsu ga yara masu tasowa.

Wani bincike da aka yi a shekarar 2019 ya nuna cewa an samu karuwar mutane masu amincewa da ‘yan madigo da luwadi – duk da cewa wadanda ba su amince da su ba sun fi yawa.

Kashi 60 cikin dari na ‘yan Najeriyar da aka yi binciken a kansu sun ce ba za su amince da wani dan uwansu ba idan dan luwadi ne ko madigo, amma wadannan alkaluman sun ragu idan aka hada da kashi 83 cikin dari a shekarar 2017.

Bukatar kawo sauyi na daga cikin abubuwan da suka sa mutane irin su Ikpe-Etim ke son ci gaba da ba da labarin masu son auren jinsi daya.

“A mtsayina na dan kungiyar da ake warewa, kullun kana cikin zullumin mutane za su yi maka mummunar fahimta.

“Na san cewa idan ina so al’uma ta ga masu sha’awar aren jinsi daya a wata hanya ta daban, dole ne in bayar da cikakken labarinsu,” a cewarta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply