Jarumar Finafinan Yarabawa, Sandra Alhassan, ta bayyana irin kalan Saurayin da zata iya kulawa, da wanda ko kallo bai isheta ba, domin ita babbar yarinya ce ba ajin Talakawa ba.
Jarumar, wacce mahaifiyarta asalin ‘yar jihar Edo ce, mahaifinta kuma dan jihar Kano, ta ce ta ki jinin Talaka kazamin saurayi, kuma mummuna.
Kyakkyawar Jarumar ta ce tana matukar son kula samari masu kyau, tsafta, aji da kuma dukiya daga kowane ?angare ba tare da la’akari da addini ko ?abila ba.
Yayin da a gefe guda kuma ta tsani munana, talakawa da kuma kazaman samari, wa?anda ke sa ta shiga cikin damuwa da ba?in ciki sakamakon ganin su, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Istagram.
“Ba zan iya sauraron kazamai, gajoji da kuma talakawan samari ba. Sannan na tsani ganin saurayi mai cike da yarinta. “Duk da ana cewa, so hana ganin laifi, amma gaskiya ina da matukar zaben samari. Idan kuwa aka zo batun aure, kankat kenan.
Muna ganin yadda ake samun matsaloli a aure; wasu har kashe junansu suke yi. “Ina shawartar ‘yan uwana mata da su kiyaye fada wa aure ba tare da sun tantance maza ba. A kula da yanayin miji kafin a kai ga yin aure. Idan mutum yayi aure, ana sa ran har karshen rayuwarsa kenan.”
A cewarta, ta rabu da saurayinta wanda ta fi so fiye da kowa saboda ta shiga harkar fim, amma mahaifiyarta ta bata kwarin guiwa. Tayi kuka matuka, amma bayan ta shiga fim, sai ta kwantar da hankali.