Duniya Na Cikin Yanayi Mafi Muni A Tarihi – Shugaban Rasha


Shugaban Rasha Vladimir Putin ya ce duniya bata taba samun kanta cikin mawuyacin hali ba tun bayan yakin duniya na biyu kamar a wannan karon.

A jawabinsa Putin ya zargi kasashen Yamma da kokarin tursasa wa duniya siyasarsu da al’adunsu.

Ya ce kasashen Turan suna so kowa ya bi salon yadda suke gudanar da rayuwa ko yana so ko baya so, wanda kuma hakan a cewarsa mulkin mallaka ne.

Putin ya ce su ne suka haddasa yakin da ke faruwa a Ukraine, kuma yana da yakinin a karshe Amurka da kawayenta za su bukaci su tattauna da Rasha.

Rahotanni na cewa abunda Putin ya kira aiki na musamman a da suke yi a Ukraine ya shiga wata na tara, kuma ya sanar a yau cewa, ba ya dana sani.

Labarai Makamanta

Leave a Reply