Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya yi Alla-wadai da harin da Iran ta kai wa Isra’ila, inda ya buƙaci dukkan ɓangarorin da su kai zuciya nesa.
“Ina kira ga dukkan ɓangarori da su kai zuciya domin guje wa duk wani abu da zai janyo yin fito na fito ta ɓangaren soji a Gabas Ta Tsakiya,” kamar yadda ya rubuta cikin wata sanarwa.
“Na sha nanata cewa yankin ko ma duniya ba za su iya jurewa shiga wani yaƙi ba.”