Duk Wanda Ya Nemi Cin Hanci Wajenku Ku Fallasa Shi – Tinubu Ga ‘Yan Kasuwar Qatar

Shugaban ?asa Bola Tinubu ya ro?i manyan masu zuba jari na ?asar Qatar cewa shi gwamnatin sa ba irin gwamnatin baya ba ce, wadda wasu jami’an gwamnati ke kar?ar cin hanci kafin su ha?a masu son zuba jari Najeriya da shugaban ?asa.

Tinubu ya ro?e su cewa ?ofa a bu?e ta ke so shigo Najeriya su zuba jari, domin akwai damammaki sosai na jiran su.

Ya ce duk wani jami’in gwamnati da ya nemi su ba shi cin hanci kafin ya ha?a su da shugaban ?asa, to su fa?a masa ko wane ne, su fallasa sa shi.

Haka ya sanar a lokacin ganawarsa da Zauren Masu Zuba Jarin Najeriya da Qatar, a Doha, babban birnin Qatar.

“Kada kowa ya bayar da cin hanci don a ha?a shi da ni a Najeriya. Idan wani ya nemi ku ba shi cin hanci, to ku sanar da ni. Haka idan ma ya kar?a, ku fa?a min. Saboda za ku samu damar gani na.

“Yanzu Najeriya ba kamar irin Najeriya ta can baya ba ce, inda ake mana kallon masu son zuba jari ba su iya ganin shugaban ?asa, sai sun bayar da cin hanci. Saboda haka kada irin wa?annan labarin da ku ka ri?a ji a gwamnatocin baya su kashe maku guyawu.

“Yanzu Najeriya vda gaske ta ke yi, muna ?o?arin samar da nagartaccen sauyi ga tsarin zuba jari. Za mu cire duk wasu tarna?i da matsalolin da masu sha’awar zuba jari ke fuskanta a Najeriya. Mun yi hakan sosai a cikin watanni tara da muka yi kan mulki.

“Don haka ina tabbatar maku cewa shigowa Najeriya a zuba jari kyauta ne, haka fita ?in ma kyauta ne. Ku?a?en za ku ri?a hada-hada a waje da ku?a?en ku a duk lokacin da ku ke so. Saboda haka ku hanzarta zuba jarin ku a Najeriya.”

Related posts

Leave a Comment