Duk Wanda Ya Ce Akwai Yunwa A Najeriya Maƙaryaci Ne – Adamu Aliyu

Ɗaya daga cikin manyan na kusa da shugaba Muhammadu Buhari kuma tsohon dan majalisar wakilai, Farouq Adamu Aliyu, ya bayyana cewa duk masu cewa akwai yunwa a Najeriya makaryata ne.

Adamu Aliyu ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin hira da yake a shirin gari ya waye (Sunrise) na tashar Channels.

Dan siyasan yace a jiharsa ta Jigawa, babu yunwa kuma hakazalika sauran jihohin Najeriya. Yayinda aka yi masa tambaya da rahoton dake nuna cewa Najeriya ce cibiyar yunwa a duniya, Adamu Aliyu yace: “Ban tunanin gaskiya ne saboda jihata da sauran jihohin Najeriya mutane basu jin yunwa.” “Karya ce kawai, a kasar nan babu yunwa.”

A bangaren guda, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen mako, ya ce gwamnatinsa bata shirya bude iyakokin kasar ba a yanzu. Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su ci abunda ake shukawa a kasar. Ya fadin hakan ne da yake amsa tambayoyi a filin Jirgin sama na Sir Ahmadu Bello, Birnin Kebbi a lokacin wani rangadi don ganin irin barnar da ambaliyar ruwa ya yi a jihar Kebbi.

Shugaban kasar wanda ya samu wakilcin ministan noma, Mohammed Sabo Nanono, ya ce a shirye gwamnatin tarayya take ta ba manoma tallafi domin bunkasa harkar noma.

Labarai Makamanta

Leave a Reply