Duk Shugaban Da Ya Gaza Wajen Samar Da Tsaro Ya Sauka Kawai -Sheik Rijiyar Lemo

Fitaccen Malamin addinin musulunci a jahar Kano Sheikh Dr Rabi’u Umar Rijiyar Lemo yayi kira ga shugabanni a kasar nan da su gaggauta shawo kan matsalar rashin tsaro wadda ta addabi yankin Arewacin Najeriya.

” Yau a kasar nan muna ganin yadda gwamnati ke cika jaha guda da jami’an tsaro saboda sha’anin zabe, amma ba za a yi haka ga jahohin da ke cikin matsalar tsaro ba, abin takaici yau idan za ka je Daura daga Kano za ka ga yadda gwamnati ta cika hanya da jami’an tsaro kawai don kar a shigo da shinkafa, idan an ga wanda ya shigo da ita a biyo shi a harbe ko a kashe, alhali ga ‘yan ta’adda can suna kashe al’umma, mutum na kwance a gidansa za a fito da shi a kashe shi, a yi wa matansa fyade a tafi da su wannan wace irin musiba ce?

Shi Shugaba nagari kasancewa yake a koyaushe cikin matsalolin jama’arsa, shi ne wanda zai fuskanci musibun al’ummarsa ya kuma tsaya ya ki yin bacci don dakile matsalolin al’ummarsa.”
Inji Dakta Rijiyar Lemo.

Sheikh Rabi’u Umar wanda yake dan uwa shakiki ga Babban Malami masanin hadisi Dakta Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemo ya kuma shawarci gwamnati da ta gaggauta janye jami’an tsaro daga wuraren da ba a bukatarsu zuwa jahohin da ke fama da matsalar tsaro a kuma basu kayan aiki.

” Ya zama lallai malamai su fito su nusar da gwamnati kan ta dauki mataki, yanayin yayi muni fiye da yadda ake zato, menene amfanin rayuwar idan har ba za a kiyaye rayukan al’umma da jininsu ba? Mutane nawa ake kashewa akan abin da bai kai ya kawo ba? Mutum nawa jami’an tsaro suka kashe akan naira ishirin ko hamsin amma ba za a dau mataki ba amma an bar ‘yan ta’adda na kashe mutane, yau ka ji an kashe goma gobe ishirin jibi hamsin, an kashe an kwashe da yawa kai kace ba rayukan jama’a ake kashewa ba, ga mutane suna mutuwa da yunwa shugabanni suna shakatawa yadda suke so ko a jikinsu ba sa ji, shin me za su gaya wa Allah?

Babu lallai ba dole, duk shugaban da ya ga ba zai iya kare rayukan al’umma ba ya sauka kawai, ko ba komai zai iya kubuta a wajen Allah.

Abu zarri R’A babban Sahabi ne mai girma, yana da takawa da gaskiya ya nemi Annabi S.A W ya ba shi aiki, Annabi ya ce masa ya na da rauni, domin ita amana tabewa ce da nadama gobe kiyama idan har mutum bai rike ta da gaskiya ba.

Wannan Hadisi ya shafi kowa har da shugaban kasa da sauran shugabannin tsaro, idan ba za ka iya ba kawai ka kauce, a yanayin da ake ciki kamata yayi shugabanni su koma inda wannan matsala take su tare har sai an magance ta, rayuwa ita ce ta fi komai muhimmanci, shugabanni ba su sama mana tsaron ba, ba kuma su sama mana komai ba, muna fadawa shugabanni su gyara a sanda suke da dama tun kafin damar ta kubuce musu nadama ta biyo baya.”

Inji Dakta Rabi’u Umar Rijiyar Lemo A Yayin Gabatar Da Sallar Juma’a A Birnin Kano

Related posts

Leave a Comment