Duk Ranar Da Buhari Ya Bar Mulki Sai Talakawa Sun Yi Kuka – Shugaban Manoma

Alhaji Shuaibu Wakili, Shugaban kungiyar masu noman shinkafa na jihar Katsina, ya bayyana cewa tun da ake mulki a Nijeriya, ba’a taba samun Shugaban Kasa da ya kula da rayuwar talakka ba, kamar ta shugaban kasa Muhammadu Buhari a irin kokarin tallafawa Kungiyoyin manoma a kasar nan, idan da ace za’a iya gyaran kundin mulki, Ina goyan bayan ya zarce ya zama Shugaban Kasa na din-din, saboda duk ranar da ya bar mulki, wallahi talakkawan sai sun yi kuka da idanun su a kasar nan.

Alhaji Shuaibu Wakili, ya bayyana haka ne a lokacin ya ke tattaunawa da manema labarai, a Ofishinsa da ke titin Ibrahim Babangida, cikin garin Katsina.

Shugaban Manoman Shinkafa, ya ci gaba da cewa duk wanda ya ce akwai yunwa a kasar nan a mulki Buhari to ya dai fadi ra’ayin sa ne kawai, amma ba gaskiya ba ne. A lokacin da aka yi yunwa duk yawan Katsina shago daya ko biyu ke da abinci, a yanzu haka ne? Amma na yadda a kasar nan akwai talauci, tattalin arziki na duniya ne ya kare ba Nijeriya kadai ba ce.

Alhaji Shuaibu Wakili ya kara da cewa sakamakon irin yadda gwamnatin tarayya ke tallafawa manoma masu noman abinci daban daban. Idan da ana gyaran kundin tsarin mulki a kasar nan, wanda zai baiwa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari damar ya zama Shugaban Kasa na din-din, mu manoman shinkafa da sauran kungiyoyin masu noma kayan abinci, wallahi za mu goyi bayan shi dari bisa dari, Saboda mu dai manoma ba irin taimakon da ba ta yi mana ba. A Kaka ana saida buhun masara dubu goma sha shida, ba’a taba ba, sai wannan gwamnati, haka manomi na gona abi ka da kudi da taki a baka, idan manomi bai godewa gwamnatin Buhari ba, ya saurari azabar Allah.

Da ya juya kan matsalar tsaro, ya ce matsalar tsaro gadon ta muka yi a gwamnatin baya, kuma duk abinda Shugaban kasa Buhari ya kamata ya yi shi, wani lokaci har da mutanen gari ake hadawa a yi wannan ta’addanci, dole sai mun dage da addu’o’i ga gwamnati na ganin ta kawo karshen sa.

Daga karshe, Shugaban Manoman Shinkafa, ya goyi baya bude kan iyakokin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi, tun da har yanzu ba abinci za’a dunga shigo da shi ba. Amma mun ji dadi da aka ce ban da abinci, ta karfafa mana gwiwar a fito a Yi noma kuma tuni al’umma suka amsa kiran. Mun shirya tsaf domin yin wani shiri da za mu yi dalar shinkafa. Shinkafar da muka noma ba ta da sinadari na daban, wadda ake shigowa da ita ana iya ajiye ta shekara biyar kuma sinadari ake sanya mata, shi ya sa ciwuka suka yi yawa a tsakanin al’umma. Mutane sama da dubu dari suka amfana da bashin noman shinkafa da gwamnatin tarayya ta baiwa Manoman shinkafa a jihar Katsina. Baa taba gwamnati da take daukar kudi taba manoma shinkafa da masara da rogo da kuma manoman kifi kusan kowa an bashi duk karkashin jagorancin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari. Kukan da yan Nijeriya dama sun saba, sun yi lokacin Babangida da Abacha daga baya sun yabe su, wallahi duk ranar da Buhari ya bar mulki, sai talakkawan kasar nan sun yi kuka da idanun su, musamman manoma.

Labarai Makamanta