Duk Lauyan Da Ya Tsayawa Wanda Ya Zagi Annabi Ya Kafirta – Sheikh Mabera

Shugaban Majalisar malamai na kungiyar Izala reshen jihar Sokoto, Sheikh Abubakar Usman Mabera kuma babban limamin masallacin Juma’a na Malam Buhari Dan Shehu dake Sokoto, ya yi kira ga musulman da ke kokarin bada kariya ga wanda kotu ta yankewa hukuncin kisa a jihar Kano sanadiyar ya zagi Manzon Allah SAW cewa su sani hakan zai iya sa su rasa addininsu na musulunci.

Sheikh mabera ya tabbatar da cewa duk wanda ya yi kariya ga wannan asararren mutumin to ya sani shi ma ya kafirta.

Saboda haka Babban Limamin ke kira ga wadanda ke kokarin sa kansu cikin wannan lamari su shiga taitayinsu.

Daga karshe ya jawo hankalin al’umma da su koma ga Allah domin shi dai ne zai iya fitar da mu wannan hali na kuncin rayuwa da muka samu kanmu ciki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply