Rahotanni sun bayyana cewa, sama da makiyaya 4,000 sun sauka a yankin Ladduga dake cikin karamar hukumar Kachia ta jihar Kaduna tun bayan fara barazanar korarsu daga yankin kudancin kasar nan.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa makiyayan da suka sauka a yankin, ana zargin cewa suna cikin Fulanin da rikicin yankin kudancin Kaduna ya tarwatsa ne.
Munyi iya bakin kokarin mu wurin jin ta bakin Ardon Ladduga Raguni Pate akan batun, wani mazaunin yankin Mohammed Iliya ya bayyana cewa tun bayan haramtawa fulanin zaman yankin kudu suka fara dawowa wasu akan ababen hawa wasu kuma a kasa tare da dabbobinsu.
“Za ka tausaya musu in ka ga halin da suke ciki musamman mata da yara kanana, an kashe wasu da dabbobinsu an lalata gidajensu, yanzu haka a waje suke kwana kuma muna tsammanin wasu ma na kan hanyar dawowa” a cewarsa.
Ya bayyana cewa wakilan hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna (SEMA) sun ziyarci yankin tare da daukar kididdigarsu da kuma alkawarin kawo musu tallafi.
Mataimakin Daraktan Hukumar ta SEMA Hussaini Abdullahi da ya ziyarci Ladduga ya ce fulanin sun haura 4,000 kuma ana ci gaba da daukar kididdigarsu.
Shugaban Miyetti Allah na jihar Haruna Usman Tugga ya shaida cewa suna shirin kai musu ziyara don ganin halin da fulanin ke ciki.