Dubai Ta Dakatar Da Ba ‘Yan Najeriya Biza

Hukumar shige da fice ta kasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa ta bayyana dakatar da bai wa ‘yan Najeriya biza, saboda wasu matsaloli da suka shafi diplomasiyya tsakanin kasashen biyu.

A wata sanarwa da suka aike wa kamfanonin shirya tafiye-tafiye a Najeriya ranar Juma’a, hukumomin kasar ta UAE sun ce ”duka takardun neman izinin biza da aka cike an dakatar da su yanzu”.

An ruwaito gwamnatin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa na cewa duka wadanda suka cika takardun neman biza za a mayar musu da takardunsu ba tare da samun amincewa ba.

Ta kuma ce ”kin amincewar ya shafi kowanne dan Najeriya, dan haka babu wanda za a ba shi biza a halin yanzu”.

Ta kara da cewa dakatarwar za ta ci gaba ne zuwa lokacin da za ta sulhunta da gwamnatin Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply