Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar hukumar tsaron farin kaya a DSS, ta tabbatar da cewa an kama mai kamfanin jaridar Desert Herald, wanda kuma yake shiga tsakani don kubutar da fasinjojin jirgin kasa da ‘yan bindiga suka sace daga Abuja zuwa Kaduna.
Sanarwar da jami’in yada labarai na hukumar DSS, Peter Afunanya, ya aike wa manema labarai, ta ce ‘yan sandan kasa da kasa na kasar a Masar su ne suka kama Tukur Mamu a filin jirgin sama a birnin Al-khahira ranar 6 ga watan nan, lokacin yana kan hanyarsa ta zuwa kasar Saudiyya.
Sanarwar ta ce an dawo da shi Najeriya ranar Laraba 7 ga watan Satumba, kuma yana hannun DSS inda ake gudanar da bincike akansa.
Hakan na zuwa ne bayan rundunar soji, da fannin shari’a sun bukaci abokan huldarsu na kasashen waje su dawo da Mamu gida domin amsa tarin tambayoyin da jami’an tsaron Najeriya ke son ya amsa musu, masu alaka da batutuwan tsaro da kasar ke fama da su.