DSS Ta Bankaɗo Shirin Tayar Da Rikicin Addini A Jihohin Najeriya

Hukumar jami’an tsaro ta farin kaya DSS ta bayyana cewa ta bankaɗo wasu mutane na kokarin tada wutar rikicin addini a wasu Jihohin kasar nan a kowanne lokaci daga yanzu.

A wata takarda da ta fito daga hannun kakakin hukumar DSS, Dr. Peter Afunanya, ya tabbatar da cewa jami’ansu suna kokarin shawo kan lamurran domin bai wa ‘yan Najeriya kariya, cikin gaggawa.

Takardar wacce aka rarraba ta ga manema labarai a birnin tarayya Abuja ranar Litinin, ta lissafa jihohin da masu son tada tarzomar suka mayar da hankali.

Jihohin sun hada da jihohin: Sokoto, Kano, Kaduna, Plateau, Rivers, Oyo, Lagos da wasu Jihohi dake sashen kudu maso gabashin Najeriya.

“Daga cikin shirinsu shine yin amfani da ɓata gari wurin kai hari wuraren bauta, shugabannin addinai, manyan mutane da sauransu. “A domin haka ake shawartar ‘yan Najeriya da su kasance masu kulawa da gujewa irin wadannan mutane.

“Yayin da hukumar take kokarin ganin ta hada kai da sauran hukumomin tsaron wurin tabbatar da zaman lafiya, tana shawartar masu wannan yunkurin da su guji aikata hakan domin tabbatar da zaman lafiya.

“Amma kuma ana shawartar ‘yan kasa nagari da kuma sauran jama’a da su kai rahoton duk wani karantsaye na zaman lafiya ga hukumar tsaro mafi kusa,”.

Labarai Makamanta