DSS Ne Suka Kama Yaron Wajena – Tanko Yakasai

Mahaifin Salihu Tanko korarrren Hadimin Gwamnan Kano Ganduje Alhaji Tanko Yakasai, ya tabbatar wa manema labarai cewa ba garkuwa da dan sa aka yi ba, jami’an tsaro na farin kaya ne, SSS suka arce da shi Abuja.

Tanko Yakasai ya kara da cewar babu kokwanto ko shakka a cikin maganar da ya keyi, dalili kuwa sun yi bankwana da ?an nashi lokacin da ya shaida mishi zai tafi ya yi aski, kwatsam sai ga wannan labarin na cewar wai wasu mutane sun yi gaba da shi.

Dattijo Yakasai ya cigaba da cewar ya sani zai wahala ?an nashi ya ?ore a gwamnatin Ganduje sakamakon yadda ya yi fice wajen fa?in gaskiya komai dacin ta akan muradun gwamnati.

Tun bayan kama Salihu Yakasai da SSS suka yi da safiyar Asabar aka rika zargin ko masu garkuwa da mutane ne suka arce da shi.

Duk da gashi hadimin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko kan ragargaji gwamnatin Buhari da salon mulkin shugaba Buhari.

Salihu Tanko ya ragargaji Buhari da jam’iyyar APC a lokacin da ya rubuta cewa jam’iyyar sa, APC ta gaza, ta yaudari ‘Yan Najeriya ne rashin iya kawo karshen matsalar rashin tsaro da ame fama da shi a kasar.

Salihu ya ce ” Da ma fa talakawan Najeriya sun zabe mu ne domin a kawo musu karshen matsalar rashin tsaro da kasar ke fama dashi amma kuma maimakon sauki tabarbarewa da muni abin yayi.

” Ace wai a kullum aka tashi sai an kwashi mutane da sunan an yi garkuwa da su, abu kamar almara. Idan ba zaka iya ba ka hakura mana ka tattara ka yi tafiyar ka. Abin ya muni matuka.

Idan ba a manta ba, ranar Juma’a mahara suka kwashe daliban makarantar sakandare a Jangebe, jihar Zamfara.

Ba wannan ne karon farko da Salihu Tanko, ke ragargazar gwamnatin Buhari ba. A baya da ya yi irin haka gwamnan Kano Ganduje ya dakatar da shi da ga ci gaba da yi masa hidima, sai dai daga baya ya dawo da shi.

Related posts

Leave a Comment