Don Allah Ku Daina Yi Wa Matasa Aski – Shehu Sani Ga Hisbah

Tsohon Sanata daga jahar Kaduna Comrd Shehu Sani yayi kira ga hukumar Hisba a jahar Kano data daina yiwa matasa askin karfi saboda suna tara gashi.

Shehu Sani ya bayyana cewa tara gashi ra’ayi ne, kuma babu wata doka a Najeriya data haramta tara gashi, don haka a kyale matasa su ajiye gashin su matukar su na da ra’ayin yin hakan.

Hakama Shehu Sani ya kara da cewa zai ja kunnuwan matasa masu tara gashi dasu dinga tsaftarsa tareda gyaran shi kamar yanda ya kamata.

Labarai Makamanta

Leave a Reply