Dokar Zabe: Fadar Shugaban Kasa Ta Maka Majalisa Kotu

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Shugaba Muhammadu Buhari da Ministan Shari’a Abubakar Malami, sun garzaya Kotun ?oli, su na neman a yi masu fassara da sharhin ma’anar wani sashe na Sabuwar Dokar Za?e ta 2022.

Buhari da Malami sun shigar da ?arar tun a ranar 29 Ga Afrilu, inda su ka maka Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya kotu.

Sashe na 84(12) na Sabuwar Dokar Za?e dai ya shiga harankazamar ja-in-ja a Najeriya, tun bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Sabuwar Dokar Za?e ta 2022 hannu cikin watan Fabrairu.

Jim ka?an bayan Buhari ya sa wa ?udirin dokar hannu ta zama doka, ya ro?i Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa cewa su soke wancan sashe da ake ta tankiya a kan sa, amma su ka yi ?ememe, su ka ?i goge shi.

Abin Da Sashe Na 84(12) Ya ?unsa:

“An haramta wa mai ri?e da mu?amin siyasa ko mu?amin gwamnati ko shugabancin jam’iyya yin za?e a matsayin wakilin masu za?en ‘yan takara. Kuma ba a yarda a za?e shi ba, sai da idan ya ajiye mu?amin sa.”

Related posts

Leave a Comment