Dokar Soshiyal Midiya: Za A Kai Gwamnoni Gaban ?uliya

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta SERAP ta yi barazanar maka majalisar dokokin Nijeriya da kungiyar gwamnonin Arewa a kotu, matukar aka kirkiro da wata doka kan kafafen intanet kuma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya mata hannu.

SERAP ta fadi haka ne a cikin wani sakon twitter da ta wallafa a shafinta, ranar Talata, kan matakin gwamnonin Arewan na son ganin an sa ido ga kafafen sada zumuntar bayan abun da ya faru daga zanga-zangar EndSARS.

A cewar SERAP, ‘yan Nijeriya na da ‘yancin fadar albarkacin bakinsu a intanet a don haka babu dalilin danne masu wannan hakkin.

Related posts

Leave a Comment