Muhmmadu Sannusi II, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), ya ce Naira za ta cigaba da rasa daraja matukar ‘yan Najeriya basu rage kwadayinsu na son yin amfani da kayan da ake shigo dasu daga ketare ba.
Sau biyu CBN ta na karya darajar Naira a shekarar 2020; a karon farko ta mayar da farashin $1 ya koma N360 daga N306 sannan ta sake mayar da farashin $1 ya koma N380.
Sunusi ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da ‘yan jaridu a birnin Ikko.
Tsohon Sarkin na Kano ya ce har yanzu Najeriya ba ta gina tattalin arziki mai karfin gaske da ya dace da ita ba. Ya ce Najeriya ta na shigo da kayayyaki daga kasashen ketare bayan za a iya samar dasu a cikin gida.
Sanusi ya dora laifin matasalolin tattalin arzikin Najeriya a kan dogaro da man fetur lamarin da ya sa gwamnatocin baya su ka sakankance, ga shi yanzu hakan ya taba tattalin arzikin kasa.
“Da ma can an dora Najeriya a turbar da za ta sha wuya, saboda fiye da kaso 90 na kudin shiga da gwamnati ke samu ya na fitowa ne daga cinikin man fetur, shi kuma farashinsa hawa yake yana sauka. “Mu danyen man fetur muke samarwa, amma kuma alhakinmu ne mu saka farashin man fetur da aka shigo da shi bayan an tace, ta yaya za ka tsayar da farashin kayan da ba kai kake sayowa ba?.
Ɗanyen mai muke samarwa ba tataccen man fetur ba. “Mu ne kadai kasar da keda arzikin man fetur amma ba ma cin moriyar hauhawar farashin danyen man fetur a kasuwar duniya saboda ba ma tace danyen mai a cikin gida, sai an siyo daga kasar waje,” a cewar Sanusi.
Ƙwararren masanin tattalin arzikin ya bayyana cewa Naira za ta fi samun daraja idan Najeriya ta hada kai da kasashen nahiyar Afrika ta yamma wajen tace danyen man fetur a gida. Kazalika, Sanusi ya yabawa gwamnatin mai ci a kan wallafa rahoton bayanin kudaden da NNPC ta kashe wanda shine irinsa na farko a shekara 20.
“Ba zai yiwu a iya farfado da darajar Naira ba sai mun rage dogaro da kuma mayatar son amfani da kayayyakin da ake shigowa dasu daga waje. “Domin tabbatar da hakan akwai bukatar samun hadin kai a tsakanin kasashen nahiyar Afrika a kan daina siyo duk wasu kayayyaki daga ketare matukar za a iya samarwa ko sarrafasu a gida.
“Dole a samu wannan amincewa a tsakanin kasashen nahiyar Afrika ta yamma, saboda koda CBN ya hana a shigo da wasu da kayayyaki sai ma’aikatar kasuwanci ta yi nata aikin, musamman aiki tare da sauran makwabtan kasashe.
“Hatta kayan da za mu iya samarwa a gida shigo dasu ake yi. Ba ina nufin cewa mu fara kera motoci, jiragen sama yanzu ba, abubuwan da zamu iya samarwa ya kamata mu mayar da hankali wajen samar dasu da sarrafasu. “Hakan zai taimaka wajen samar da aiyuka, gina tattalin arzikin kasa, da daga darajar takardar Naira,” a cewarsa.