Dogaro Da Kai: Ana Horas Da Matasa 200 Sana’o’i A Kaduna

Kungiyar samar da zaman lafiya da inganta lafiya (e-CAPH) da ha?in gwiwar ?ungiyar taimakon al’umma (RCCE) ?ar?ashin shirin raya ?asa na majalisar dinkin duniya, sun fara aiwatar da horas da matasa 200 sana’o’i domin dogaro da kai a Jihar Kaduna.

Shirin ya fara da matasa 20 ne daga yankin Gundumar Rigasa gunduma mafi girma a yankin ?aramar Hukumar igabi ta jihar Kaduna.

Shugaban Kungiyar ta e-CAPH Malam Yusha’u Abubakar ya sanar da haka ga manema labarai a yayin kaddamar da zagaye na farko da matasa 20.

“Akwai mutum 12 masu fama da nakasa wa?anda aka sanya su cikin tsarin domin cin gajiyar shirin”.

Yusha’u Abubakar ya kara da cewar wannan yana cikin shirin horas da matasa 200 sana’o’i daban daban wadanda suka ha?a da yin amawali na gargajiya, da zannuwan gado da takalma da sauransu.

“Ana sa ran zango na farko za su kware akan wadannan abubuwa har ya zamana sun kai ga matakin koya ma wadansu anan gaba.

“Muna fatan hakan zai taimaka su wajen dogaro da kula da kai, da kuma kaucewa shiga dukkanin wadansu abubuwa da basu kamata ba.

Related posts

Leave a Comment