Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Dawowar Buhari Najeriya: Bai Shafi Tafiyar Shi Landan Ba – Fadar Shugaban Ƙasa

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar, Shugaban ƙasa Buhari ya dawo Najeriya bayan tafiyar da ya yi kasar Kenya, da fari an tsara Shugaban zai wuce Birnin Landan daga Nairobi domin ganin Likita.

Sai dai Fadar Shugaban ƙasa ta yi ƙarin haske akan dawowarsa inda tace Tafiyar Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, zuwa Landan domin ganin likita ta na nan a ranar Lahadi mai zuwa.

Mutane sun yi mamakin ganin shugaban ƙasan ya dawo gida Najeriya ranar Jumu’a, maimakon zarcewa Birnin Landan kamar yadda fadarsa ta sanar.

Amma da aka tuntubi babban mai taimaka wa shugaban ƙasa ta bangaren watsa labarai, Malam Garba Shehu, ya ce Buhari ya dawo Najeriya ne bayan kammala aikin da ya je Nairobi da wuri.

“A’a, bai soke tafiya Landan ba, shirin na na kamar yadda aka tsara. Ya kammala abin da ya kai shi Kenya shiyasa aka ga ya dawo gida. Tafiya Landan na nan ranar Lahadi.”

Buhari ya halarci bikin cikar shirin majalisar dinkin duniya (UNEP) karo na 50 a Nairobi Kenya, da nufin wucewa Landan na tsawon mako biyo domin a duba lafiyarsa. Hadimin Buhari, Femi Adesina, shi ne ya bayyana shirin tafiya Landan na farko, a wata sanarwa da ya fitar a farkon makon da muke ciki.

Exit mobile version