Dauke Wutar Lantarki Ya Tursasa Majalisar Kasa Dage Zama

Labarin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar ɗaukewar wutar lantarki bagatatan, ana tsaka da zaman muhawara a Majalisar Wakilan Najeriya, ya tilasta wa zauren ɗage zamansa ranar Talata.

An ruwaito cewa shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila ne, ya sanar da dage zaman bayan majalisar ta auka cikin duhu rana tsaka.

Lamarin ya tilastawa ‘yan majalisar fita daga zauren majalisar cikin duhu, har ma wasu sun rika amfani da fitilun wayoyinsu.

Katsewar lantarki a kai-a kai babbar matsala ce da ke addabar sassan Najeriya inda ko a ranar Litinin sai da babban layin lantarki na kasar ya fadi, abin da ya janyo daukewar wuta a kusan illahirin kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply