Rahotanni daga Jihar Legas cibiyar al’ummar Yarbawa na bayyana cewar An aika sako ga mai rajin ballewar Yarbawa daga Najeriya, Sunday Adeyemo Igboho da aka fi sani da Sunday Igboho.
Sakon wanda Kungiyar Walwalar Yarbawa (YWG) ce ta aiko dashi, na bayyana cewar: – ya dauki darasi daga abinda ya faru da Nnamdi Kanu jagoran Tsagerun Inyamurai.
Wannan na zuwa ne yayin da Igboho ke dagewa kan cewa babu gudu babu ja da baya a ranar Asabar, 3 ga watan Yuli cewa sai ya gudanar da taron Yarbawa a jihar Legas.
Shugaban kungiyar, Kwamared Abdulhakeem Alawuje ya shawarci Igboho da kada ya tsunduma kansa cikin ayyukan da za su jefa yankin kudu maso yamma cikin rikici kamar yadda ake gani a yankin kudu maso gabas. Ya ce:
“Tare da duk goyon bayan da Kanu ya yi ikirarin yana da shi, an kama shi kamar kaza kuma an dawo da shi Najeriya ba tare da wata hayaniya ba. A yanzu da muke magana, ana ci gaba da shari’arsa a babbar kotun Abuja.”