Dangote Ya Karya Farashin Man Dizel

A wani yunkuri na rage wahalhalun da ?an Nijeriya ke fuskanta, matatar man Aliko Dangote ta sanar da ?ara rage farashin man dizel daga naira 1200 zuwa 1,000 kan kowacce lita.

A cikin wata sanarwar da kamfanin ya fitar ranar Talata ya ce ana sa ran ”rage farashin man dizel ?in zai yi tasiri sosai a dukkan ?angarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.”

A watan Janairu ne matatar man Dangote ta fara samar da man dizel da na jiragen sama.

Tun daga lokacin matatar take sayar da man dizel a kan farashi mai rahusa na Naira 1,200 a kowace lita, kimanin kashi 30 cikin 100 na ragin farashin kasuwa da ya kai kusan Naira 1,600 kan kowace lita.

A ranar 12 ga watan Disamba 2023 ne kamfanin ya amshin jirgin ?anyen mansa na farko daga ?anyen mai na Agbami na kamfanin Shell International Trading and Shipping Company Limited (STASCO), ?aya daga cikin manyan kamfanonin kasuwanci a Nijeriya da ma duniya baki ?aya, wanda ke cinikin ?anyen mai sama da ganga miliyan 8 a wacce rana.

Kamfanin ya ?aura ?amarar fara samar da tataccen man fetur tare da samun ?arin ganga miliyan ?aya na ?anyen man da Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC Ltd) ya kawo.

A farkon watan ne kamfanin ya fara fitar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida.

Related posts

Leave a Comment