DAMULEWAR NIJERIYA: SHIN ‘YAN NIJERIYA ZASU IYA GYARA KASAR SU?
………………
Ahmed Ilallah

Abin takaici ne halin da nijeriya ta ke ciki na damulewa daga gazawar yaki da cin hanci da rashawa, lalacewar tsaro, rashin tsarin tattalin arziki da ciyar da Nijeriya gaba, uwa uba rushewar ilimin irin na jami’a, wanda shine ke bada tsarin da kowace kasa ta kan hau wajen cigaban ta. Ko ba komai, yau ta nuna wa kowa yadda ginin wannan kasa ke narkewa kadan-kadan, amma jagororin wannan kasar hankalin su yafi karkata wajen siyasar su, ta yadda kawai zasu dawwama a kan karagar mulki da tara dukiya ta ko yaya, a gefe guda kuma al’umar kasar na sake duruwa cikin kogin talauchi da takaici.

Halin da kasar nan take ciki a yau, tabbas zai saka shakkun kokarin yan Nijeriya wajen gyaran wannan kasa. Buhari da APC sun sami nasarar darewa karagar mulkin Nijeriya bisa gagarumin campaign da alkawuran da suka yi wa yan Nijeriya na gina tattalin arzikin wannan kasa, yaki da cin hanci da rashawa, kasancewar rashawa ce babbar annobar da tayi wa wannan kasa tarnaki na ci gaba, samawa kasar nan tsaro bisa la’akari da barazanar da Boko Haram ta ke yiwa wanna kasa, kawo gyara da ci gaban ilimi, musamman kawo karshen yawan yajin aikin malaman jami’oin wannan kasa. Amma a yau yaya kasar nan take ciki, musamman game da wadannan matsaloli?

Cin Hanci da Rashawa, shine babban ciwon da ya hana kasar nan bunkasa, shine babban linzamin da yake ruruta gudun rashin tsaro da yake addabar wannan kasar, musamman ma yankin arewa cin kasar nan. Gazawar wannan gwamnatin na kawo chanji a yakin da ake da cin hanci da rashewa ya kawo shakkun cewa, shin yan Nijeriya kuwa zasu iya gyara kasar su?

Kafin muyi duba, da maganganun da ke yawo a yau, na dacewar yin afuwar da Shugaba Buhari yayi wa wasu tsoffin gowamnoni da kotu ta hukunta bisa laifin rashawa ko akassin haka, shafewa da mayin da aka yi wa wasu takororin su da suke fuskantar irin wadan nan shari’oi wanda a yau sune jagorori a wannan gwamnati, kuma masu fada a ji, a gwamnatin da ke ikirarin ita ce kan gaba wajen yakar cin hanci da rashawa, tabbas abin mamaki ne da ma sanya ayar tambaya akan nagartar wannan mulki, yin kallo na nutsuwa da irin rikon sakainar kashin da shugabanni suke yi wa su kan su Hukumomin da suke yaki da cin hanci da rashawa mafa abin tambaya ne.

Shin rigimar da faru tsakanin Ministan shari’a Malami, da tsohon shugaban EFCC Ibrahim Magu, har ya kai da cire shi a mukamin sa, ya banbanta ne da irin danbarwar da aka samu lokacin tsohon Shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua tsakin Ministan Shari’ar sa a wannan lokacin da tsohon shugaban hukumar EFCC wato Malam Nuhu Ribadu, yanayin rigimar suna da kamanceceniya da juna, a takaice siyasa tafi tasiri cikin rigimar, fiye da kishin kasa da kuma inganta yaki da cin hancin da rashawar domin ceto Nijeriya, irrin wannan halayya tabbas na nuna shakku ko yan Nijeriya na iya gyara kasar su. Wannan ya nuna karara babu wani banbanci a kan wannan matsalar tsakanin PDPn jiya da APCn yau.

Afuwar su Dariye da kokonto shugaba Buhari akan yaki da cin hanci da rashawa. Bisa duba ta nutsuwa akwai abubuwa da ya kamata a hankalta su, wa yanda suka hada da.

Joshua Dariye da Jolly Nyame su kadai ne gwamnonin da aka kai ga hukuntawa duk da kasan cewar akwai takwarorin su da yawa da ake tuhuma akan irin wannan badagala, misali irin su shugaban APC Senator Abdullahi Adamu, Senator Danjuma Goje, abin tambaya ya matsayin irin wadannan tsoffin gwamnoni yake a yau?

An rusa tunanin yan Nijeriya, an kauda tunanin su wajen kishin kasa, an raba tunanin su a kan bangaranci, banbancin addini. Nijeriya an kasa ta tsakanin ‘Yan Arewa Hausa Fulani, wanda akasari musulmi ne, ‘Yan Arewa Minority ko Middle Belt, akasari kiritoci ne, Yarabawa, ‘Yan Igbo, su Igbo da Yarabawa basa nuna banbancin addini a tsakanin su. Joshua da Jolly wa yanda Buhari yayi wa afuwa Kiristocin Arewa ne, wanda hakan na nuna cewa, kamar an zabi wata kabila ne kawai a ka yankewa irin wannan hukunci yayin da aka kauda kai ga wasu masu irin wannan laifi da suka fito da ga wasu yanku nan, na kin yi musu irin wannan hukuncin duk da an gurfanar da su a gaban kuliya, amma ana cewa ita shari’ a abace mai rikidar wa. Wannan tunani kadai ya isa yayi wa kasar nan tirnaki cigaba. Amma, watakila irin wannan nazari ne ya sanya Shugaba Buhari yayi musu afuwa.

Matsalar ASUU da taki ci taki cinye wa a tsawon shekaru, irin wannan matsala a Nijeriya kadai take, babu wata kasa da al’umar suke da kishi zasu aminta da irin wannan matsala. Duk kasashen da suka ci gaba a kowa ne fanni sun dogara ne da ilimi, bicike da tunani jami’ oin su wajen gina tubulin ci gaban su.

Babu ko shakka rashin shugaban ci, ilimi da kyakkyawan tunani ya sanya Nijeriya a baya tsakanin takororinta, duk albarkar gonakin mu da yawan jama’ar mu, mun kasa noma abin cin da zamu ciyar da kasar mu, mun kasa samarwa kasar mu wutar lantarki, duk da yaduwar ilimi da fasaha cikin sauki da duniya ta samar, abin takaici ne mun kasa sarrafa man fetur da iskar gas domin amfanin mu duka da arzikin da Allah ya bamu a wannan fannin.

A yau talauchi ya kai mutuka, ‘Yan Nijeriya basu da karfin saye da sayar na muhimman abubuwan bukatun su, kananan chututtuka kullum na kashe ‘Yan Nijeriya saboda rashin kudin sayen magani, ta’addanci, masifu sun yawaita saboda tsannanin talauchi. Babban tashin hankalin shine dabarun sun karewa masu mulki wajen yaye wa al’ummar wannan kasa mummuna yanayin da suke ciki.

A yau babu kasar da kai Nijeriya rashin kwanciyar hankali, musamman ma arewacin ta, kullum asarar rai ake, sace mutane a ke, kasar nan na neman zama dandalin safarar miyagun kwayoyi da masifu kala kala.

Koma mene ne ya kamata muyi wa kan mu tambaya, shin zamu iya gyara kasar mu? Ba a aiko mana shugabanni da ga wata duniya, a cikin mu ake fidda shugabanni, ya zama dole sai mun gyaru zamu iya gyara kasarmu, sai mu fifita kasar mu a kan duk wata bukatar mu zamu iya gyara kasar mu, mu kauda talauchi, rashin tsaro, cin hanci da rashawa, sannan mu gina kasar mu.

Tabbas rashin rike amanar masu mulki na wajen sauke nauyin da suka dauka, da kykkyawan tunani, ragon taka, kishin kasa da sadaukar wa ya zama kalubale ga shugabannin wannan kasa.

alhajilallah@gmail.com

Labarai Makamanta

Leave a Reply