Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Damka Jagorancin APC Ga Matawalle Ya Bar Baya Da Kura

Rahotanni daga Jihar Zamfara na bayyana cewar Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, da Sanata Kabiru Marafa, sun yi tur da batun cewa Gwamna Bello Matawalle ne shugaban APC a jihar.

Jiga-jigan na Jam’iyya mai mulki sun bayyana hakan ne a wata hira da sashin Hausa na BBC a ranar Laraba, 30 ga watan Yuni jim kaɗan bayan shugaban kwamitin rikon Jam’iyyar Mai Mala Buni ya ayyana Gwamna Matawalle a matsayin jagoran Jam’iyyar a jihar.

Idan za ku tuna, Shugaban riko na APC, Mai Mala Buni ya ayyana Gwamna Matawalle a matsayin jagoran jam’iyyar a jihar Zamfara bayan ya sauya sheka daga PDP.

Sai dai kuma Yari da Marafa sun nuna adawa da jagorancin jam’iyyar da aka damka wa Matawalle, inda suka ce hakan ba mai yiwuwa bane. “Abu guda ne ba mu lamunta da shi ba, inda Buni ya ce Matawalle ne shugaban APC saboda a lokacin da muka tattauna da gwamnoni guda shida babu shi a ciki.

“Abunda muka aminta da shi shine a je a kaddamar da Bello a dawo. Amma da muka je an yi takkadama mun tarar da an yi tsari in ji wasu cewa idan an je a ruguza jam’iyya. Ba a rushe jam’iyya ba domin babu wanda ke da ikon ruguza ta,” in ji Yari.

A bangaren Marafa ya ce daura Gwamna Matawalle a matsayin shugaban APC a Zamfara wata yaudara ce da ba su yarda da ita ba. Ya jadadda cewa zancen banza da wofi ne wani ya zauna a Abuja ya ce ya ruguza jam’iyya tare da nada wani shugaba.

A gefe guda, Asiwaju Bola Tinubu, babban jigon APC na kasa, ya yi wa gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, maraba da zuwa jam’iyyar mai mulki. Tsohon gwamnan na Legas ya yaba wa Matawalle kan yadda bai mika wuya ga tursasawa da matsin lamba da jam’iyyar PDP ta yi masa don hana shi sauya shekar ba.

Exit mobile version