Dambarwar Sarautar Kano: Kotun Tarayya Ta Jingine Nadin Muhammadu Sanusi ll

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Kano na bayyana cewa a ranar jiya Alhamis ce Mai Shari’a A. M Liman ya yanke hukuncin cewa kotu ta jingine naɗin Sarki Muhammadu Sanusi II kuma ta hana Gwamnatin Jihar Kano rushe Masarautu biyar da ya yi.

Mai Shari’a ya ce ba daidai ba ne a ƙi bin umarnin kotu tun da farko.

A ranar Laraba ce Fitaccen Lauya Femi Falana ya ce Babbar Kotun Tarayya ba ta da ikon tsoma baki cikin lamarin masarautu, wanda hurumi ne da iko na Gwamna da ‘Yan Majalisa na Jiha.

Tun ranar Laraba dai Gwamnatin Kano ta shigar da ƙara ta na neman Kotun Ɗaukaka Ƙara ta karɓi shari’ar, domin ta na zargin rashin adalci.

Yanzu kuma za a jira hukuncin Babbar Kotun Kano domin a ji na ta hukuncin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply