Gwamnatin Kano kar?ashin Abba Kabir Yusuf ta ce hukuncin babbar kotun tarayya ya ?ara tabbatar da tu?e Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hu?u, tare da tabbatar da sarautar sarki Sanusi.
Ta ce daga nan zuwa lokacin da kotun ?aukaka ?ara za ta yi hukuncin, Aminu Bayero da sauran sarakuna hu?u za su ci gaba da zama a matsayin wa?anda aka sauke.
Sakataren watsa labarai na mai girma gwamnan Kano, Sanusi Bature ne ya bayyana haka a wata hira da Channels tv cikin shirin siyasa a ranar Jumu’a.
“Ya kamata mutane su fahimci cewa hukuncin ya nuna muke da nasara saboda dalilai da dama. Na farko kotu ta amince da ingancin dokar masarauta ta 2024. “Hakan na nufin ta amince da rusa masarautu biyar tare da tsige sarakuna biyar na Kano.” “Saboda haka idan muka yi la’akari da hukuncin, ta tabbata an tu?e rawanin Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna hu?u har zuwa lokacin da za a yi hukunci a ?arar da muka ?aukaka.”
Idan baku manta ba mai shari’a Liman na babbar kotun tarayya ya soke duk matakan da gwamna ya ?auka bayan fara aiki da sabuwar dokar masarauta 2024.
Amma a cewarsa, hukuncinsa bai shafi dokar ba illa iyaka ya soke duk abin da Abba Kabir ya yi wajen aiwatar da ita kamar dawo da Sanusi II.
To sai dai a fassarar Bature, tun da har al?alin bai haramta dokar ba, to ya tabbata cewa Muhammadu Sanusi II ne sahihin Sarkin Kano.