Dambarwar Sarautar Kano: Gwamnatin Kano Ta Zargi ‘Yan Sanda Da Nuna Bangaranci

IMG 20240524 WA0093

Gwamnatin jihar Kano ta zargi ƴan sanda a jihar da nuna ɓangaranci a dambarwar masarautar da taki ci taki cinyewa a jihar.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Mal Sunusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan yayin wata hira da tashar Talabijin ta Channels a ranar Juma’a.

Dawakin Tofa ya bayyana muhimmancin dawo da martabar sarautar kano da ya zargi tsohuwar Gwamnatin Ganduje da rusawa.

A hannu guda kuma gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin da ta gabace shi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.

Yayin da yake jawabi a gabanin taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar ranar Asabar a fadar gwamnatin jihar, Gwamnan Abba Kabir ya nuna damuwarsa kan halin taɓarɓarewar tsaro da jihar ke fuskanta, musamman harkar dabanci.

”Kowa ya sani kafin mu shigo gwamnati, waccan gwamnatin da ta shuɗe ita ce ke ɗaukar nauyin ‘yan daba, ita ce ke sa su suna yin abin da duk suka ga dama suna cutar da al’umma”, in ji gwamnan na Kano.

Gwamnan ya kuma ce a lokacin yaƙin neman zaɓensa ya yi alƙawarin kakkaɓe matsalar daba a Kano.

Ya kuma ce bayan nasararsa a zaɓen gwamnatinsa ta yi ƙoƙarin daƙile matsalar.

Amma ya ce a cikin wata biyu da suka gabata wasu da ya kira ”maƙiyan jihar” suka maido da harkar daba.

Inda ya yi zargin cewa wasu sun ɗauko hayar wasu ‘yan daba daga makwabtan jihohi domin su kawo wa zaman lafiyar jihar cikas.

Abba Kabir ya kuma yi barazanar fara kiran sunayen mutane da yake zargi da ɗaukar nauyin ‘yan daba a jihar.

Haka kuma gwamnan ya nuna damuwarsa kan yadda ya ce wasu na zuwa ofishin ‘yansanda domin fito da ‘yan daba idan hukuma ta kama su.

Inda ya yi barazanar cewa duk mutumin da gwamnatinsa ta sake samu da wannan laifi to za a gurfanar da shi a gaban kotu, domin yin bayanin dalilinsa na ɗaukar nauyin ‘yan daba a Kano.

A baya-bayan nan dai jihar Kano na fuskantar faɗace-faɗacen ‘yan daba, waɗanda ke cin karensu babu babbaka a wasu unguwannin jihar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply