Dalilina Na Ziyartar Tsohon Shugaban Kasa Buhari – Atiku

IMG 20240316 WA0103

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023 a ƙarƙashin jam’iyyar PDP ya kai ziyarar ne tare da rakiyar wasu manyan abokan siyasarsa.

A saƙon da Atiku Abubkar ya wallafa a shafinsa na X, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya ce ya kai wa tsohon shugaban Najeriyar ziyara ne domin yin ”gaisuwar Sallah”

Ziyarar ta Atiku Abubakar ta zo ne kwana uku bayan ya ziyarci tsaffin shugabannin Najeriya, Ibrahim Babangida da kuma Abdulsalami Abubakar a gidajen su da ke jihar Niger.

Ana dai alaƙanta irin wannan ziyara da shirye shiryen babban zaɓen 2027.

Labarai Makamanta

Leave a Reply