Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Dalilina Na Kin Bin Matawalle Jam’iyyar APC – Mataimakin Gwamnan Zamfara

Mataimakin Gwamnan Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya bayyana wa BBC matsayinsa, inda ya ce yana nan daram a jam’iyyarsa ta PDP bayan gwamna Bello Matawalle ya sauya sheƙa zuwa Jam’iyyar APC a ranar Talata.

“Tun asali a nan nake tun mahaifi na ya kawo jam’iyyar ba mu taba barin PDP ba, nan aka same mu kuma nan za mu tabbata,” in ji shi.

Mahdi Aliyu Gusau ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin jam’iyyarsa ta PDP na garzayawa kotu domin ƙwatar kujerarta ta gwamna da kotun ƙoli ta najeriya ta ba ta, tare fatan mulki zai dawo hannunsa.

Duk da mataimakin gwamnan na Zamfara ya ce babu wata matsala tsakaninsa da gwamna Bello Matawalle amma ya ce gwamnan bai nemi shawararsa ba har zuwa lokacin da ya yi wanka zuwa jam’iyyar APC.

Exit mobile version