Labarin dake shigo mana daga Minna babban birnin Jihar Neja na bayyana cewar tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya bayyana cewa matan wannan zamani basu kaunar aure da fuska ta tsofaffi sun fi ƙaunar yara.
Babangida ya faɗi hakane yayin wata hira da kafar watsa labarai ta Arice TV a gidansa dake Minna, babban birnin jihar Neja ranar Jumu’a.
A yayin hirar tasa, tsohon shugaban ya yi tsokaci a kan wasu muhimman batutuwa da suka haɗa da tattalin arziki, siyasa, tsaro da kuma halin da ƙasa ke ciki musamman a wannan lokaci na mulkin Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A lokacin da aka kawo batun Maryam, marigayya matarsa, tsohon janar ɗin sojojin ya yi murumushi. Da aka tambayeshi meyasa bai sake aure ba tun bayan mutuwar matarsa a 2009? cikin raha IBB ya amsa tambayar da cewa: “Matan yanzun basu kaunar fuskata.” Cikn hanzari ya kara bayani da cewa: “Ba abune mai sauki ba gaskiya, haka Allah ya so.”
Daga nan kuma sai ya fara bada takaitaccen tarihin yadda suka haɗu har ya auri marigayya matarsa, wadda suka haifi ‘yaya huɗu. IBB yace: “A lokacin yakin basasa 1969 na samu raunuka sosai Ozokuli jihar Abia, daganan sai na dawo Lagos duk da ba abune mai sauki ba amma Allah ya taimake ni.”
“Janar Gawon ya yi aure a tsakanin wannan lokacin Afrilu ko Mayu, kuma shine jagorana kwamanda na. A lokacin na yi sha’awar yadda aurensu ya kasance.” “Ina gadon asibiti lokacin sai na tambayi kaina, da fa yanzun na mutu da bazan yi aure ba kenan kamar yadda shugabana yayi. Anan na yanke cewa da zaran na samu lafiya aure zan fara yi kafin komai. Kuma da taimakon Allah na warke.”
IBB ya kara da cewa a wancan lokacin nayi sa’a matar da zan aura da iyalanta duk sun amince da ni, Tsohon shugaban yace: “Na santa sosai, ina yawan shiga gidansu a kan wasu dalilai saboda haka mun saba da yan uwanta mun zama kamar abokai.” “Lokacin da na nemi aurenta ban samu wani kalubale ba kowa ya amince. Bayan watanni kalilan aka ɗaura mana aure.”