Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Dalilin Kotu Na Bada Umarnin Tura Shugaban EFCC Gidan Yari

Rahoton dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar wata babbar kotun tarayya ta samu shugaban hukumar ya?i da cin hanci da rashawa ta ?asa EFCC Abdulrasheed Bawa da laifin sa?a wa umurnin kotu, a wani hukunci da ta yanke a 2018.

A hukuncin da ya yanke ranar Talata, mai shari’a Chizoba Oji ya ce hukumar ta EFCC ta ?i aiwatar da wani hukuncin da kotu ta yanke a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018, inda ta umurci hukumar da ta mayar wa wani mutum motarsa kirar Range Rover da ku?i naira miliyan 40.

Kotun ta bu?aci da a tura shugaban hukumar ta EFCC gidan yari har sai ya wanke kansa daga laifin.

Haka nan kotun ta bu?aci sifeta janar na ?an sandan Najeriya ya tabbatar an aiwatar da hukuncin.

Wanda hukuncin na shekarar 2018 ya bu?aci da a mayar wa kayan nasa ne ya shigar da ?ara, inda yake zargin hukumar da ?in bin umurnin da kotu ta bayar a hukuncin na farko.

Exit mobile version