Labarin dake shigo mana daga jihar Kano na bayyana cewar Mutumin da ake zargi da kashe wata budurwa a Kano ?an ?asar Chaina Geng ya yi zargin cewa Ummu ta masa al?awarin zata aure shi amma daga baya ta sa?a al?awarin bayan ya kashe ma?udan ku?i a kanta.
A jawabin da ya yi wa yan sanda, ?an China ya bayyana cewa sa?a al?awarin ya fusata shi sosai, bisa haka zuciyarsa ta raya masa ya je har gida ya kasheta.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan Sandan Jihar Kano Kiyawa ya ?ara da cewa Mahaifiyar yarinyar ce ta rinka kururuwar neman taimako lokacin da Geng ke aikata ?anyen aikin kuma nan take aka sanar da yan sanda suka kai ?auki.
Tuni dai kwamishinan yan sanda ya umarci DPO na Caji Ofis ?in ?orayi Babba ya kula da lamarin, inji Kakakin yan sandan Kano.
Bayanai sun bayyana cewa a halin yanzun an maida ?an Chinan sashin binciken mayan laifuka na Hedkwatar yan sanda dake Bampai, Kano domin tsananta bincike da kuma mi?a shi Kotu.
A ?aya ?angaren kuma, tuni aka Sallaci marigayya Ummu Kulthum aka kaita makwancinta ranar Asabar da Safe yayin da yan uwa da abokanan Arziki ke jimamin rasuwarta.