Ministar harkokin kuɗaɗe Zainab Ahmed ta bayyana cewa babu wata mafita sai Najeriya ta ciwo bashi sannan ta ke iya yin ayyukan raya ƙasa.
Zainab na fito ƙarara ta bayyana wannan mawuyacin halin da Najeriya ke ciki ne, yayin da ta ke jawabi a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai ta ƙasa mai Lura da harkokin kuɗaɗe, a ranar Laraba.
Ta bayyana gaban kwamitin tare da Daraktan Ofishin Lura da Basussuka, wato DMO, Ben Akabueze, Akanta Janar na Tarayya na riƙo, Okolieboh Sylva da wasu jami’ai.
Ta ce zuwa watan Agustan da ya gabata bashin da aka ciwo ya kai naira tiriliyan 5.33, saboda haka ya zarce ƙa’idar gejin adadin da ya kamata a ciwo bashi da naira biliyan 430.82.
Ta ce a cikin Yuli kuwa bashin ya zarce geji da naira tiriliyan 1.26.
Najeriya ta sake yin sabon shirin ciwo bashin naira tiriliyan 8.2 domin wasu daga ayyukan da ke ƙunshe cikin kasafin 2023.
Idan za a tuna kuma, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC Bola Tinubu, ya bayyana cewa bashin da gwamnatin Buhari ta ciwo ba shi da illa, duk cikin aiki ne.
Tinubu ya ce tulin bashin da Buhari ya ciwo ba illa ba ce, duk cikin aikin ne.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a ya bayyana cewa masu aibata Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnatin sa saboda sun ciwo bashi, ba su yin zurfin tunani.
Tinubu ya ce yawan bashin da Gwamantin Buhari ta ciwo ko ya ke kan ciwowa, ba illa ba ce, domin ayyukan raya ƙasa ake yi da kuɗaɗen.
Ya yi wannan furucin a lokacin da Buhari ke ƙaddamar da Kwamitin Kamfen ɗin TInubu da Shettima a Abuja.
A wurin Ƙaddamarwa, Shugaba Muhammadu Buhari ya jaddada cewa rayukan ‘yan Najeriya za su fi garantin samun kyakkyawar kulawa a hannun APC fiye da sauran jam’iyyu masu takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Buhari ya ce ya zama wajibi a yi duk irin ƙoƙarin da ya dace domin a ga APC ta ci gaba da mulki, yadda ‘yan Najeriya za su ci gaba da cin alherin da APC ta kawo a ƙasar nan.
Yayin da ya ke jinjina wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, Buhari ya kuma jinjina wa dukkan sauran ‘yan takarar da su ka yi zaɓen fidda gwani tare da Tinubu, amma su ka janye masa, ko kuma ya kayar da su.
Ya ce babu wata jam’iyyar da ta dace da ‘yan Najeriya sai APC.
Da ya ke jawabi, Tinubu ya jinjina wa Buhari da kuma gwamnatin sa, tare da cewa idan ya hau mulki, zai ɗora daga inda Gwamnatin Buhari ta tsaya.
An dai ƙaddamar da Daftarin Ƙudirorin APC, wato APC manifesto, mai shafuka 80, wanda cike ya ke da wasu alƙawurran da APC ta ɗauka tun a 2015, amma har yau ba ta cika ba.
Shugaban Kamfen ɗin TInubu 2023, Gwamna Simon Lalong na Jihar Filato, ya ce ya zama wajibi duk wani ɗan kwamitin kamfen ya tashi tsaye wurjanjan ya yi aiki tuƙuru.