Dalilin Cireni A Shirin Kwana Casa’in – Safara’u

Jarumar Finafinan Hausa ta Kannywood, da ke fitowa a shirin ‘Kwana Casa’in’, Safiyya Yusuf wadda aka fi sani da Safara’u ta sanar da dalilin da yasa aka canja ta da wata jaruma ta daban a shirin mai farin jini.

Jaruma Safiyya Yusuf ta ce rashin lafiya ne ya kwantar da ita ta gaza zuwa a cigaba da shirin da ita don haka aka maye gurbinta da wata.
“Wannan shine gaskiyar lamari saɓanin labaran ƙanzon kurege da wasu jama’a ke yaɗawa akai”.

Jarumar mai farin jini ta kuma bayyana sabon shirin da ta ke yi a yanzu mai suna ‘Kaddarar So’ wanda ta bayyana cewar zai gamsar gami da ƙayatar da jama’a idan ya fito aka fara nuna shi a gidajen Kallo.

Jaruma Safiyya Yusuf wacce ta yi fice saboda rawar da ta taka a cikin sanannen shirin talabijin mai suna ‘Kwana Casa’in’ da ake nuna wa kowanne mako a Arewa 24, ta yi wadannan bayanai ne a wata tattaunawa da Jaridar Daily Trust.

A cewar Safiyya, “an maye gurbina ne da wata ne a shirin saboda ina ta fama da rashin lafiya sosai a wannan lokacin ake ɗaukar fim har ta kai bana iya zuwa wurin aiki”

“An fara daukan sabbin shirin ban samu zuwa ba saboda rashin lafiyar don haka basu da wani zabi ila su maye gurbi na a wannan lokacin.”

Jarumar ta fara bayyana cewa ta fito ne a matsayin yarinya wacce ta dage ta yi karatu har da zama likita a shirin. Mahaifiyarta na fama da matsanancin ciwon kafa don haka ta ke son ta zama likita don ta taimaka mata da ma wasu mutanen.

A bangarensa mahaifinta shi kuma baya son ta da karatun, so kawai ya keyi ta yi aure domin ya samu kudi daga manema auren.

Labarai Makamanta

Leave a Reply