Gwamna Babagana Zulum na Jihar Barno ya nuna farin cikin sa dangane da ci gaban da jihar sa ke samu wajen ?arfafa tsaro. Sannan kuma ya yi addu’a Allah ya sa tsaron ya fi yanzu ?aruwa a cikin 2022.
A sa?on murnar shiga sabuwar shekara da gwamnan ya fitar a ranar Asabar, Zulum ya ce gwamnatin sa za ta ci gaba ?ara yin ho??asan ganin an kawo ?arshen matsalar tsaro a Jihar Barno.
Daga nan kuma Zulum ya kare tare da bayar da hujjojin dalilan su na rufe sansanonin masu gudun hijira.
“Tilas su yarda cewa sai da rai ake samun abincin da za a rayu. Muna aiki ba dare ba rana domin ganin an wanzar da zaman lafiya wanda za mu iya bai wa jama’a garanti cewa za su iya fita neman abincin su cikin kwanciyar hankali.
“Cikin 2021 mun yi ?o?ari tu?uru wajen ?ara wa jami’an tsaron mu ?arfi, har ma da ‘yan bijilante wa?anda muka bai wa kayan aiki da ku?a?en da za su yi ayyukan su sosai.
“Mun ga alfanun wannan ?o?arin cikin 2021, domin a shekarar ba a samu muggan hare-hare ba. Kuma sojojin mu sun yi rawar gani sosai.
“Duk da haka dai ba mu kai har inda muke son ganin mun kai wajen samar tsaro ba, amma dai mu na samun ci gaba sosai. Don haka ina mai tabbatar maku cewa na sadaukar da kai na wajen bayar da goyon baya ga dukkan ?angarorin jami’an tsaron mu da jajirtattun ‘yan bijilante ?in mu wa?anda ke taimaka mana.” Inji Zulum.
Da ya ke magana kan kwashe ‘yan gudun hijira ana maida su yankunan garuruwan su, tare da rufe sansanonin, Zulum ya ce ana yin haka ne domin a dawo wa mutane da martabar su sai kuma dalilai na da?ile ?arnar da ya ce ta ke faruwa a cikin sansanonin.
Zulum ya lissafa ba?alar da ake yi a cikin sansanonin sun ha?a da karuwanci, sace-sace da shan muggan ?wayoyi a cikin sansanonin masu gudun hijira.
Zulum ya ce gwamnatin sa na sake tsugunar da jama’a a bisa tsarin da duniya ta yarda da shi, kuma ake yi a duk duniya. Sannan kuma ya na tanadar masu da kayan tallafi idan sun koma mazaunan su.
“Gwamnatin mu ta fi fifita al’ummar Jihar Barno, domin mutanen mu su ne ha??in su ya rataya a wuyan mu.
“Mu na sane da cewa za su ri?a cin karo da ‘yan matsaloli ko ?alubale yayin da su ka koma garuruwan su, ko inda aka sake tsugunar da su. Dalili kenan mu ke samar masu da tallafi iri daban-daban, domin ?ara masu ?warin guiwar zama a muhallan su.”
Zulum ya ce matsalar wutar lantarki a Maiduguri da kewaye na nan ana ?o?arin shawo kan aikin Tashar Samar da Gas a Maiduguri, wadda ya ce Gwamnatin Tarayya ta kusa kammala aikin nan ba da da?ewa ba.