Dalilan Da Ya Sa Muka Yanyanka Manoma A ?auyen Zabarmari – Boko Haram

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani faifen bidiyo da take bayyana cewa ita ke da alhakin kai hari tare da hallaka manoman shinkafa fiye da 40 a kauyen Kosheba da ke Zabarmari a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Ta kuma ce ta hallaka manoman ne saboda sun kama wasu dakarunta inda suka mika su a hannun sojojin Najeriya da ke gudanar da aiki a yankin.

Da ma dai tun bayan da aka kai harin mutane da dama suka fara zargin cewa mayakan na Boko Haram ne suka aikata.

Hakan kuma baya rasa nasaba da yadda ‘yan kungiyar suka dade suna kai irin wadannan hare-hare a yankunan daban-daban na jihar Bornon.

A ranar Asabar din da ta gabata ne maharan suka kai farmaki cikin gonakin a yankin Koshebe na kauyen Zabarmari da ke ?aramar Hukumar Mafa a jihar Borno inda suka kashe fiye da mutum 40 ta hanyar yi musu yankan rago.

Galibin wadanda maharan suka kashe dai an datse kawunan na su ne.

Wasu mazauna yankin sun tabbatar wa da BBC ce, maharan sun abka wa manoman ne yayin da suke girbin shinkafa.

Related posts

Leave a Comment