Dalilan Da Ya Sa Muka Kai Buhari Kotu – Gwamnoni

Sababbin karin bayanai sun kara fitowa game da dalilin da ya sa gwamnonin jihohi 36 su ka shigar da gwamnatin tarayya kara a gaban kotun koli.

A lokacin da shugaban kasa ya sa hannu a doka mai lamba ta 10, ya dogara ne da sashe na 5 da na 121 (3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

A dokar kasa, kotun koli ce ta ke da ikon raba gardama tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi. Da wannan doka da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo, ana sa rai kotuna za su fi samun cikakken ikon aiwatar da duk ayyukansu kai-tsaye.

Kamar yadda Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya bayyana, za a rika zare kudin kotunan jihohi kai tsaye daga cikin kudin gwamnati na FAAC.

Hakan ya na nufin duk jihar da ta ki fitar wa bangaren shari’a kudinta, gwamnatin tarayya za ta dauki mataki da kanta, ta zare wannan kudi daga asusu.

Gwamnoni sun ce wannan sabuwar doka ta ci karo da wasu sassa na kundin tsarin mulki, domin gwamnatin tarayya ke dawainiya da kotunan tarayya.

Haka zalika shugaban kasa aka bar wa nauyin kotunan daukaka kara, da manyan kotunan shari’a.

Gwamnonin jihohi sun kai karar gwamnatin tarayya ne ta hannun Austin Alegeh SAN da wasu manyan Lauyoyi, daga ciki har da masu mukamin SAN.

Wata lauyar da ta tsayawa jihohi, Chinweoke Onumonu, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bar gwamnoni da wahalar kudin da kotuna su ke batarwa. Bayan albashin da gwamnatin tarayya ta ke warewa Lauyoyi ta karkashin majalisar NJC, gwamnonin su na kukan an bar su da tarin dawainiya.

Dawainiyar da gwamnonin su ka ce su na yi sun hada da gina dakunan shari’a, gidajen Alkalai da sayen kayan aiki, tare da sayen motoci da dai sauransu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply