Fadar shugaban kasa ta bayyana dalilan da suka sanya aka sallami hafsoshin tsaro a ranar Talata inda ta bayyana cewar an dauki matakin sauke su ne ba wai don sun gaza ba, sai dai domin sauya fasalin tafiyar da tsaro a kasar.
Fadar Shugaban Kasa ta kara da cewa an yi hakan ne a wannan lokacin domin kara karfi a fannin yaki da ta’addanci tare da shawo kan matsalolin tsaro a kasar nan, waɗanda suka daɗe suna addabar ƙasar.
Mai ba Shugaban Kasa shawara na musamman a fannin yada labarai Femi Adesina ya sanar da hakan a wata zantawa da yayi da gidan Talabijin na Channels TV a kan harkar tsaro da siyasa a ranar Talata.
“Abinda yasa aka sauke su a yau ba yana nufin sun gaza bane a gaskiya ba hakan bane. Kawai ana son sabbin jini ne da kuma sabbin dabarun yaki a kasar nan,”
“A takardar da shugaban kasar ya fitar a ranar Talata, ya jinjinawa hafsoshin tsaron da suka tafi a kan gudumawar da suka bada wurin tsaron kasar nan. Ya gamsu da ayyukansu ba kadan ba.
“Wadannan hafsoshi da suka sauka a yau sun kasance a kujerunsu na tsawon shekaru biyar da watanni biyar, lamarin na tafiya ne bisa ga tsari a lokacin da ya dace,”
Sauke shugabannin tsaron dai ya zama wani babban lamari da jama’ar ƙasar baki daya suka mayar da hankali wajen tattaunawa da zura idon domin ganin kamun ludayin sabbin Shugabannin tsaron.