Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Dalilan Cancantar Sanata Uba Sani A Gwamnan Jihar Kaduna (1)

Daga Ibrahim Ibrahim

ƊAN takarar zama gwamnan Jihar Kaduna a jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani jajirtacce ne a wurin gudanar da aiki, taimakon jama’a, kawo ci-gaba ga al’umma tun kafin ya samu damar zama sanatan Kaduna ta tsakiya.

Sanata Uba Sani mutum ne da ya kasance mai tausayin al’umma, wanda duk inda ya yi aiki sai da ya aje abin a yaba masa tare da jinjina.

Kamar yadda kowa ya sani Sanata Uba Sani ya taka rawar gani a tsawon shekaru huɗu da ya yi a matsayin sanatan Kaduna ta tsakiya.

A yau har ta kai shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kira ga al’ummar jihar Kaduna da su yi dukkanin ƙoƙarin su don ganin sun zaɓi Sanata Uba Sani a matsayin gwamnan Jihar Kaduna a zaɓe mai zuwa.

Shugaba Buharin dai ya yi wannan kira ne a lokacin da ya ke yi wa al’umma Nijeriya jawabi bayan an sanar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe shugaban ƙasa da ya gabata. Shugaban ya yi nuni da irin namijin ƙoƙarin da Sanata Uba Sani ya yi a majalisar dattijai.

Wasu daga cikin dalilan da su ka sa Sanata Uba Sani ya cancanci zama gwamnan Jihar Kaduna su ne:

*Sanata Uba Sani, ya kasance, babban jigo a fafutukar kare ‘yancin ‘yan Adam, musamman ganin cewa, a shekkarun baya, ya na ɗaya daga cikin ‘yan kare rajin da su ka yaƙi muzgunawar da sojoji su ka yi wa wasu ‘yan Nijeriya da gudunmawar da ya bayar wajen tabbatar da kafuwar mulkin dimokiradiyya a Nijeriya da a yau ake morewa.

*Sanata Uba ya taka muhimiyyar rawa a lokacin da ya ke riƙe da muƙamin mataimakin shugaba na Arewa wajen yin gangami a kan kafuwar mulkin dimokaradiya, ya kuma riƙe mataimakin shugaba na Arewa a kwamitin haɗaka na ƙungiyar (JACON) da marigayi Cif Gani Fawehinmi (SAN) ya jagoranta a lokacin yana raye.

*Kasancewar sa a matsayin shughaban kwamitin bankuna, inshora da sauran hukomomin kula da hada-hadar kuɗale na majalisar dattawa, Uba Sani ya bayar da gagarumar gudunmawa wajen gina ƙasa, inda hakan ya sa aka samu ɗimbin nasarori wajen ƙara haɓaka bankuna da hada-hadar kuɗi na Nijeriya.

*Uba Sani ya gabatar da ƙudurori guda 32 a majalisar dattawa, inda ya samu karbuwa a majalisar.

*Uba Sani shi ne Sanata ɗaya tilo a majalisa ta 9 da shugaban ƙasa ya rattaba hannun sa a kan ƙudurori biyu da ya gabatar a gaban a majalisa har su ka zama doka.

*Uba Sani a yanzu haka, shi ne sanata a kan gaba a cikin jerin sanatoci 10 a majalisa ta 9 da ya gabatar da ƙudurori a gaban majalisar dattawa.

Ga wasu da daga cikin muhimman ayyukan da Sanata Uba Sani ya gudanar a daukacin kananan hukumomin dake Jihar Kaduna, wanda a tarihi babu wani Sanatan da ya taba yin irin hakan;

Ya gina ICT center a Karamar hukumar kudan, Karamar hukumar da ‘Yan takarar Gwamnan Jihar Kaduna na Jam’iyyar PDP Isa Ashiru kudan da Sanata Hunkuyi na Jam’iyyar NNPP suka fito.

Ya taimaka wajen gina Kwalejin Injiniya ta N3.5billion a Jami’ar Jihar Kaduna (KASU). Wannan dai shi ne aiki mafi girma da Gwamnatin Tarayya ta taba yi a kowace irin jiha a Najeriya.

Ya ba da tallafin karatu ga marasa galihu 287 amma haziƙan ɗalibai a manyan makarantun gaba; Jami’ar Jihar Kaduna (KASU), Kwalejin Ilimi, Kafanchan, FCE Zariya da Nuhu Bamalli Polytechnic, Zariya.

Ya taimaka wajen gina tare da samar da cikakken kayan aikin ICT a Makarantar Sakandare ta Gwamnati, Kawo, dake Karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Ya taimaka wajen gina tare da samar da kayan aikin fasaha a Kinkinau, dake Karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Ya taimaka wajen ginawa da kuma samar da kayan aikin fasaha a Danmani, Rigasa, Karamar hukumar Igabi.

Ya taimaka wajen gina tare da samar da cikakken kayan aikin ICT a Makarantar Sakandaren Mata ta Gwamnati da ke Maimuna Gwarzo, a karamar hukumar Kaduna ta Kudu.

Ya taimaka wajen gina da samar da kayan aiki na Cibiyar ICT a unguwar Turunku, karamar hukumar Igabi.

Ya taimaka wajen gina Cibiyar Samar da Ilimi a LEA Sabon Garin Nasarawa (Tirkania) dake Karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.
Ya taimaka wajen gina katafaren dakin kwanan Dalibai mai gadaje 110 a makarantar sakandaren mata ta Shehu Lawal Giwa, dake Karamar hukumar Giwa.

Ya taimaka wajen gina katafaren dakin kwanan Dalibai mai gadaje 110 a makarantar sakandiren gwamnati (GSS), dake karamar hukumar Birnin-Gwari.

Ya taimaka wajen gina block mai dauke da ajujuwa guda 6 tare da bandaki na VIP a LEA Dan Honu 1, Millennium City, Kaduna.

Ya taimaka wajen gina block daya na ajujuwa guda 6 a Unguwar Dosa, karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Ya taimaka wajen gina tare da samar da kayan aiki na zamani a Cibiyar Kula da Mata a Babban Asibitin Birnin-Gwari.

Ya taimaka wajen gina tare da samar da kayan aiki na zamani a Cibiyar Kula da Mata a Babban Asibitin Giwa.

Za mu ci-gaba…….

Exit mobile version