Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Dalibai Za Su Fara Cin Gajiyar Bashin Karatu A Makon Gobe

images 2024 03 14T070645.613

Ɗaliban manyan makarantun gwamnatin tarayya a Najeriya da suka nemi bashin kuɗin karatu za su fara samun kuɗin nan da mako ɗaya, a cewar asusun ba da bashin ɗaliban.

Sai dai shugaban asusun, Akintunde Sawyerr, ya ce ɗaliban makarantun da za su fara sabon zangon karatu ne kawai za su ga kuɗin a asusunsu a yanzu.

A jiya Laraba ne Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da asusun mai suna Nigerian Education Loan Fund (Nelfund) a hukumance a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Mista Sawyerr ya ce jimillar ɗalibai 170,000 ne suka yi rajista da asusun, waɗanda suka ƙunshi ɗaliban jami’a, da na kwalejojin ilimi da fasaha.

“A taƙaice dai, jimillar ɗalibai 110,000 ne suka nemi bashin. Sun ba da bayanansu tare da miƙa takardun neman, kuma su ne suka cancanta. Amma duk da haka za mu ƙara gudanar da bincike a kansu… Amma da alama sama da mutum 110,000 ne za su fara samun bashin a sati mai zuwa,” in ji shi.

Exit mobile version