Rundunar sojojin Nijeriya sun bayyana cewa sun yi yi artabu da ‘yan Boko Haram a yankin ?aramar hukumar Marte dake jihar Borno.
Jaridar PRNigeria ta ce sojojin sun yi musayar wuta da ?an ta’addan a jiya Talata yayin da suka ?addamar da farmaki domin kakka?e maya?an na Boko Haram a garuruwan Hausari da Missene da Chikungudu da ke cikin ?aramar hukumar Marte.
Sai dai jaridar ta ruwaito cewa an kashe sojojin Najeriya biyu yayin da bakwai suka samu rauni.
Amma dakarun na Najeriya sun yi nasarar ?wato bindiga ?irar AK47 guda 27 da wasu manyan bindigogi masu harbo jirgin sama guda uku da motocin ya?i biyu daga hannun maya?a
Tare da hallaka mayakan na Boko haram sama da 30.
Allah ya kara baiwa sojojin Kasar mu nasara.