Yayin da ake shirin shiga yanayi na bazara a yankin arewa maso yamma, rundunar Operation Sahel Sanity ta karfafa ayyuka inda take ci gaba da kutsawa yankunan karkara don farautar yan ta’adda.
Hakazalika a tsakanin ranakun 4 zuwa 9 ga watan Oktoba, rundunar hadin gwiwa ta Operation Sahel Sanity da na Operation Hadarin Daji sun yi aikin kakkaba. Sun yi aikin ne domin gano mafakar yan bindiga a kananan hukumomin Dankar, Kandawa, Yau yau, Hayin Yau yau, Bugaje, Zandam, Kwari Mai Zurfi, Yar Gamji, Bukuru da Jaiabaiya a kananan hukumomin Batsari da Jibiya na jihar Katsina.
Hakan ya yi sanadiyar kashe yan bindiga uku, yayinda sauran suke tsere da raunuka sakamakon harbin bindiga.
Bayan arangamar, dakarun sojin sun samo mujallar bindigar AK 47 dauke da harsasai da bindigogi mallakar yan bindigan. Har ila yau sun kuma lalata baburan da mafakar yan bindiga takwas a aikin wanda ke ci gaba da gudana.