Daga Zuriyar Hausa/Fulani Na Fito – Kayode

Biyo bayan tada jijiyar wuya da ake ta yi dangane da sarautar da masarautar Shinkafi da ke Jihar Zamfara ta ba Femi Fani Kayode na Sadaukin Shinkafi, ya fito ya bayyana wa duniya nasabar shi.

Kayode ya bayyana cewar yana da alaƙa ta jini da al’ummar Hausa/Fulani, domin kakan shi wanda ya haifi mahaifinsa Hausa/Fulani ne daga daular Usmaniyya ya auri kakarshi wacce take Bayarbiya aka haifi mahaifinsa.

Kayode wanda ya yi ƙaurin suna wajen sukar Musulmi musamman Hausa/Fulani ya bayyana jin dadin shi da naɗin sarautar da masarautar Shinkafi ta yi mishi, inda ya ya yi alkawarin taimakawa masarautar da dukkanin ƙarfin shi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply