Yayin da ake fama da tabarbarewar tattalin arziki da ke kara fusata jama’a kan Gwamnatin shugaba Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasar Kashim Shettima ya zargi ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da cewa su ne ke da hannu wajen shirya zanga-zangar da za a yi a watan Agusta a fadin kasar, inda ya kira su ‘yan iska.
Da yake jawabi a wajen wani daurin aure a Maiduguri, jihar Borno a ranar Asabar, Mista Shettima ya bayyana wadanda suka shirya zanga-zangar na watan Agusta a matsayin ‘yan fashi da wawaye a ƙasashen ketare da ke kulla makarkashiyar haddasa fitina.
“Hanya daya tilo da za mu iya nuna goyon baya ga gwamna ita ce mutanenmu su guje wa raye-rayen ’yan fashi da wawaye masu tayar da barna wanda Suke zaune a kasashen Australia, Finland, da Amurka in ji Kashim Shettima.
Ya kara da cewa, “Ba a kasar nan suke ba; muna bukatar mu koyi darasi da yawa daga abin da ya faru a Siriya da Libiya. Don haka abin da suke tada hankali ne da Haifar da tarzoma a fadin ƙasar