Kungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU na shirin sake komawa yajin aiki bayan da ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarinta na biya musu bukatunsu.
A wata tattaunawa da mataimakin shugaban kungiyar da BBC ta yi, Dr Chris Piwuna, ya ce kungiyar na shirin gudanar da taron gaggawa domin yanke shawara a kan matakin da za ta dauka a cikin kwanakin nan.
‘’Za mu hadu nan gaba mambobinmu suna mana tambayoyi dole mu hadu mu san amsar da za mu ba su,’’ in ji shi.
Malaman na korafi kan yadda suka ce gwamnati ba ta biya su albashin wata takwas da suka yi suna yajin aiki ba.
Ya ce babu ko daya daga cikin alkawuran da suka yi da gwamnati ta cika.
‘’Ba su rubuta wasika sun ce sun kara mana albashinmu ba yadda muka bukaci su yi,’’ in ji shi.
Amma game da kudin bunkasa jami’o’i ya ce gwamnati ta ce za ta sa a kasafin kudi, kuma Kakakin Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila, ‘’ya nuna mana shedar yana cikin kasafin kudi.’’