Da Yiwuwar A Rage Farashin Mai A Najeriya

Kamfanin kasuwancin kayayyakin arzikin man fetur a Najeriya (PPMC) na iya rage farashin man fetur a cikin wannan watan. A hira da aka yi da mataimakin shugaban kungiyar ‘yan kasuwan man fetur masu zaman kansu IPMAN, Alhaji Abubakar Maigandu, ya bayyana cewa ‘yan kasuwan na kyautata zaton za’a rage farashin man a watan Oktoba.

Ya bayyana hasashensa ne bisa ga saukar farashin mai a kasuwar duniya. Farashin yanzu ya sauko $39.38. Amma ya ce sai kamfanin PPMC ta sanar da sabon farashin zasu fara sayarwa.

Amma hukumar lura da farashin man fetur PPPRA a watan Satumba ta ce ba farashin mai a kasuwar duniya kadai za’a duba wajen rage ko kara farashin a nan gida ba.

Idan zaku tuna cewa gwamnatin tarayya ta cire tallafin mai a watan Maris na shekaran nan. A watan Satumba, PPMC ta sanar da farashin man fetur da za’a sayarwa ‘yan kasuwan mai a N151.56 ga lita, amma ta ki fadin farashin da su ‘yan kasuwan zasu sayarwa ‘yan Najeriya.

Saboda haka, ‘yan kasuwan a fadin tarayya suka fara sayar da man tsakanin N158 da N162 ga lita.

A bangare guda, shugaba Muhammadu Buhari ya na ganin cewa babu hikima ace Najeriya ta na saida man fetur kasa da abin da ake saidawa kasashen da ke makwabtaka.

Mai girma shugaban kasar ya bayyana haka ne a jawabinsa na ranar 1 ga watan Oktoba, 2020. Buhari ya ce ba zai yiwu gwamnati ta cigaba da rike farashin fetur ba saboda halin da ake ciki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply