Da ‘Yan Kuɗi Ƙalilan Buhari Ya Yi Manyan Ayyuka A Najeriya – Lai Mohammed

Ministan yaɗa labari, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa da kuɗi kaɗan ɗin da gwamnati su ke samu ne suka yi wa ƴan Nijeriya manyan ayyukan raya ƙasa da ake gani yanzu.

Mista Lai ya bayyana haka ne a wajan da yake kaddamar da sabbin shugabannin hukumomi 9 dake ƙarkashin ma’aikatarsa, ranar Juma’a 3 ga watan satumba a Abuja.

Sannan ministan ya jawo hankalin sabbin shugabannin da su yi koyi da gwamnati wajen yin ayyuka da yawa da dan kudin da za su samu.

Ya ce gwamnati ta samu nasara sosai idan banda ma zuwan cutar Corona virus duk da ƙarancin kuɗin da take fama da shi.

Ministan ya ce ba karamin nasarori gwamnatin nasu ta samu ba, duk da bullar annobar corono virus amma hakan bai hana su yin ayyukan raya kasa ba.

Labarai Makamanta