Da Wahala A Rushe SARS – Rundunar ‘Yan Sanda

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Najeriya Frank Mba, ya ce abune mawuyaci ?ungiyar da ta san abun da take yi ta nemi a kawo ?arshen sashen hana fashi da makami (SARS).

Da yake magana game da zanga-zangar da ake gudanarwa a kan neman rushe sashen hana fashi da makami na rundunar yan sanda, Mba yace wasu daga cikin jami’an su na daga cikin masu ya?i da ta’addanci da kuma fashi a arewacin Najeriya.

Da yake magana a gidan talabijin na Channels a ranar Juma’a, Mba ya ?ora laifin zangar-zangar a kan masu cin moriyar laifuka inda ya ce wasu daga cikin masu zanga-zangar masu cin moriyar laifukan ne.

“Idan har kiran a kawo karshen sashen hana sashen fashi da makami (SARS) manuniya ce ta gyara, zan fa?i cewa shugabancin rundunar ?ansanda a shirye yake da ya kar?i kiran.
”Sai dai kuma idan kiraye-kirayen na nufin a dakatar da sashen gaba?aya, zan fa?a muku abune mayuwaci ga kowacce irin gwamnati da ta san abinda take yi ta yarda da hakan musamman idan aka yi la’akari da ma?udan ku?aden da gwamnati ta zuba wajen bada horo da kuma ?irkirar sashen, baya ga muhimmiyar rawa da sashen yake takawa.”

”Magana ta gaskiya mun kar?i kiraye kiraye da kuma ?orafi daga mutane musamman daga Maiduguri, Yobe da kuma sauran jihohin arewa inda jami’an SARS ke aiki tukuru wajen ya?i da fashi da kuma ta’addancin kungiyar Boko Haram.

“Ma su ?orafin sun bayyana cewa kawo karshen sashen ba shine mafita ba a garesu sakamakon gagarumar gudunmawar da jami’an ke bayarwa a yankin su musamman akan ?anfashi, ‘yan Boko Haram da sauran ?anta’adda da kuma sauran masu muggan laifuka,” a cewarsa.

Mba ya ce a yayin da wasu su ke damuwa game da ayyukan sashen rundunar SARS, ma su manyan laifuka na son a dakatar da sashen ne don bu?atar su cigaba da cin karen su babu babbaka.

Related posts

Leave a Comment