Da Kafar Dama Na Shigo Harkar Fim – Jaruma Sabira Mukhtar


Sabuwar jaruma da a yanzu a ke ganin nan da dan wani lokaci ita ma za ta shiga cikin sahun manyan Jarumai a Masana’antar finafinai ta kannywwod Sabira Mukhtar ta bayyana jin dadinta da irin karbuwar da ta samu tun daga lokacin da aka fara haaka Fim din Fanan wanda tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta shirya.

Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin tattaunawar su da Dimukaradiyya in da ta ke cewa.

Gaskiya tun da nake ban taba jin dadi irin na wannan lokacin da aka fara haska fim din Fanan ba, domin Sai yanzu na san mutane su na kauna ta sosai, Kuma fim din Fanan ya fito mini da daraja ta.”

“Ta ci gaba da cewa” A baya na yi finafinai masu yawa Amma ba a sanni ba, sai da na yi Fanan Kuma na fito a matsayin Jarumar fim din, don haka babu abin da zan ce Sai dai godiya ga Allah da ya sa na samu wannan daukaka wadda ta zo mini a bazata. ”

Daga karshe ta yi godiya GA Mansurah Isah wadda ta ba ta matsayin da ta fito a matsayin jaruma a fim din wanda hakan ya zamo silar daukaka a gareta. Kuma ta yi godiya da dukkan jama’ar da suka nuna Mata soyayya musamman lokacin da suka zo kallon fim din a Sinima.

Related posts

Leave a Comment